Kwallon Kwando

Najeriya ta lashe gasar kwallon Kwando a Afrika

Nigeria beat Angola in AfroBasket 2015 Final
Nigeria beat Angola in AfroBasket 2015 Final Fiba.com

‘Yan wasan kwallon kwando D Tigers na Najeriya sun lashe gasar Afrika da aka gudanar a Tunisia bayan sun doke Angola a wasan karshe ci 74 da 65.

Talla

Wannan ya ba ‘Yan wasan na Najeriya nasarar wakiltar Afrika a wasannin Olympic da za a gudanar a Brazil a badi.

Wannan ne karon farko da Najeriya ta lashe kofin gasar na kwallon Kwando a Afrika.

Tunisia ce ta zo a matsayi na uku bayan ta doke Senegal a ranar Assabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI