Isa ga babban shafi
Wasanni

An kusa daura auren Maradona da Rocio Oliva

Tsohon dan wasan kasar Argentina, Diego Maradona.
Tsohon dan wasan kasar Argentina, Diego Maradona. Reuters
Zubin rubutu: Nasiruddeen Mohammed
Minti 2

Budurwar tsohon shahararren dan wasan kwallon kafan kasar Argentina Diego Maradona, wato Rocio Oliva tace nan bada dadewa ba za a daura musu aure, duk kuwa da cewa ba a tsayar da takamammiyar ranar auren ba.

Talla

Rocio dake magana a filin jirgin saman kasar ta Argentina, jim kadan bayan da ta dawo daga Birnin Dubai na kasar hadaddiyar daular Larabawa, inda suke zaune tare da saurayin nata, tace lallai cikin wanna shekarar za ayi bukin, in hali ya samu.
Za ayi bukin Maradona mai shekaru 54, da Oliva mai shekaru 25, a fadar fafaroma ta Vatican ne, inda kuma ake sa rai Paparoma Francis, da shima mai sha’awar kwallon kafa ne, zai sanya albarka a aure.
Yanzu haka Maradona na rigima a kotu, da tsohuwar matarsa Claudia Villafane da ya saka a shekarar 2003, bayan dama ta haifa masa ‘ya ‘ya 2.
Yana kuma da wani yara maza 2 da kuma diya mace daya, da wasu mata daba suka haifa masa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.