Isa ga babban shafi
Wasanni

Rooney ya kafa wa Ingila sabon tarihin cin kwallaye

Wayne Rooney
Wayne Rooney Action Images/Reuters/Carl Recine
Zubin rubutu: Nasiruddeen Mohammed
Minti 1

Jiya Talata dan wasan kasar Ingila Wayne Rooney ya zarta yawan kwallayen da duk wani dan wasa ya taba ciyo wa kasar Ingila, bayan da ya jefa kwllonsa ta 50 a wasan da kasar tayi a gida da Switzerland, a wasannin neman shiga gasar cin kofin nahiyar Turai aka kuma tashi ci 2 da 0.

Talla

Dama Bobby Charlton ne ya kafa wannan tarihin tun shekaru 45 da suka gabata.
Rooney da shine kaftin din ‘yan wasan na Ingila, yaci kwallon ne bayan kasar tasu ta sami bugu daga kai sai mai tsaron gida, baya da kuma dama Harry Kane ya bude fagen cin kwallayen.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.