Isa ga babban shafi
wasanni

Yarima Ali na Jordan zai tsaya takarar shugabancin FIFA

Yarima Ali bin Hussaina na Jordan
Yarima Ali bin Hussaina na Jordan AFP PHOTO / ADRIAN DENNIS
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
Minti 1

Yarima Ali bin Hussain na Jordan ya bayyana sabuwar aniyarsa ta neman kujerar shugabancin hukumar kwallon kafa ta duniya wadda a yanzu ke karkashin jagorancin Sepp Blatter.

Talla

Yarima Ali ya ce shi kadai ne zai iya tinkarar matsalar cin hancin da rashawa da suka addabi hukumar ta FIFA tare da magance ta.

A watan Mayun da ya gabata Yarima Ali ya kalubalanci Sepp Blatter a zaben da aka gudanar, to sai dai gabanin kammala zaben ne ya janye, kuma daga bisani Blatter ya lashe zaben.

To sai dai a yanzu Yariman yana bukatar ya kammala abinda ya fara a farko na Kalubalantan Blatter kamar yadda ya shaidawa magoya bayansa a yau laraba da suka hada da Firai Ministan Kasar Jordan Abdullah Nsur.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.