Isa ga babban shafi
Wasanni

Tsohon gwamnan Abia Orji Kalu zai tsaya takarar shugabancin FIFA

Ginin Hukumar FIFA a Zurich
Ginin Hukumar FIFA a Zurich REUTERS/Ruben Sprich/Files
Zubin rubutu: Abdoulkarim Ibrahim
Minti 1

Tsohon gwmanan jihar Abia a tarayyar Najeriya Orji Uzor Kalu ya ce zai tsaya takarar neman shugabancin hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA.

Talla

Kalu wanda shahrarren dan kasuwa ne a bangaren harkar mai da iskar gaz, ya ce yanzu haka ya shirya tsaf domin gabatar da takararsa a zaben shugabancin hukumar da za a yi nan gaba, a daidai lokacin da rikicin karbar rashawa ya dabaibaye hukumar ta FIFA.

Ko baya ga Orji Kalu, akwai wani dan Najeriya da ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a zaben, to sai dai hukuma kwallon kafar Najeriya NFF ta ce sai dan takarar da ya cika ka’idoji kawai ne za ta mara wa baya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.