Isa ga babban shafi
Wasanni

Messi zai yi jinyar watannin biyu

Lionel Messi ya samu rauni a wasan da Barcelona ta ci Las Palmas 2-1
Lionel Messi ya samu rauni a wasan da Barcelona ta ci Las Palmas 2-1 REUTERS/Sergio Perez
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
Minti 2

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona za ta kasance ba tare da gwarzan dan wasanta ba Lionel Messi har na tsawon watanni biyu sakamakon jinyar da ya fara bayan ya samu rauni a kafarsa ta hagu a wasan da Barcelona ta ci Las Palmas 2 da 1 a karshen makon daya gabata.

Talla

Dan wasan ya samu raunin ne jim kadan da soma wasan, lamarin daya sa aka fitar da shi daga filin wasa yayin da Luis Suarez ya ja ragama har suka yi nasara.

Yanzu haka Barcelona za ta yi wasanni takwas ba tare da Messi ba kuma a gobe talata ne za ta kece raini da Bayern Leverkusen, yayin da ake ganin Bayern Leverkusen za ta iya taka rawar gani saboda rashin Lionel Messi.

To sai dai akwai Suarez da Neyma na Barcelona kuma su ake sa ran su kara kaimi a tsakanin wannan lokacin da Barcelona zata kasance ba tare da Messi ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.