Isa ga babban shafi
Wasanni

Wenger ya sha caccaka kan rashin nasara a wasa

Kocin Arsenal Arsène Wenger.
Kocin Arsenal Arsène Wenger. Reuters
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 Minti

Sakamakon nasarar da Olympiakos ta samu kan Arsenal da ci 3-2 a wasansu na jiya a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, Kocin Asrenal, Arsene Wenger ya sha suka daga magoya bayan kungiyarsa, inda suka dora laifin rasahin nasarar a kansa yayin da suka nuna rashin gamsuwarsu da zabin da ya yi na ‘Yan wasa.

Talla

To sai dai Wenger bai amince cewa yana da laifi ba, inda ya ce, aikinsa ne ya zabi 'yan wasan da zasu buga masa tamaula, kuma ya san abubuwa da dama da mutane basu sani ba dangane da zabin da ya yi.

Kungiyar Arsenal dai ba ta taba yin rashin nasarar ba a wasannin fako har guda biyu a gasar cin kofin zakakrun Turai sai a wannan karan.

Ko a makwanni biyu da suka gabata Dinamo Zagreb ta doke ta da ci 2-1 kuma a yanzu haka Arsenal ce ke kasan teburi wajan maki a rukunin da take ciki na F yayin da Bayern Munch ke jan ragama a rukunin da maki 6 sai Dainamo Zagreb da Olympikos dake da maki uku uku.

Nan gaba dai akwai wasannin biyu da Arsenal za ta yi  da Bayern Munich.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.