Isa ga babban shafi
Wasanni

Hayatou na jagorantar FIFA cikin rashin lafiya

Mukaddashin shugaban hukumar FIFA, Issa Hayatou.
Mukaddashin shugaban hukumar FIFA, Issa Hayatou. AFP PHOTO / FADEL SENNA
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 min

Mukaddashin shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Issa Hayatou ya bayyana cewa zai iya jagorantar hukumar ta FIFA duk da rashin lafiyar da ya dade yana fama da shi.

Talla

Hayatou dai na fama da matsalar koda yayin da wata sanarwa da ta fito daga hukumar kwallon kafa ta Afrika ta ce, wannan matsalar ba ta hana shi jagorancin hukumar kwallon kafa ta Afrika ba, don haka, ba za ta hana shi gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyansa ba a matsayinsa na shuganban FIFA na wucen gadi.

Hayatou mai shekaru 69 ya karbi ragamar shugabancin FIFA ne a dai-dai lokacin da zarge zargen cin hanci da rashawa suka yi wa hukumar katutu, lamarin da ya sa aka dakatar da Sepp Blatter a matsayin shugabanta har na tsawon watanni uku.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.