Isa ga babban shafi
Wasanni

Kasashe za su juya wa Platini baya

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai, Michel Platini.
Shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai, Michel Platini. REUTERS/Olivier Pon/Files

Kasashe da dama za su janye daga marawa shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai Michel Platini baya, dangane da kokarinsa na neman shugabancin hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA.

Talla

Kasashen za su yi haka ne matukar ba su gamsu ba game da kudaden da ake zargin Platini da karba daga hannun Sepp Blatter ba bisa ka’ida ba.

Ana zargin Platini da karbar sama da Pam miliyan 1 daga hannun Blatter shekaru hudu da suka gabata, lamarin da ya sa aka dakatar da su har na tsawon watanni uku.

Ana sa ran mambobin hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai  54 za su gudanar da taro a yau alhamis a kasar Switzerland domin tattauna wa kan matsalar cin hanci da rashawa da ta addabi hukumar kwallon kafa ta duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.