Wasanni

Najeriya za ta kara da Brazil a gasar cin kofin duniya

'Yan wasan Golden Eaglet na Najeriya a Chile.
'Yan wasan Golden Eaglet na Najeriya a Chile. FIFA/FIFA via Getty Images

Sakamon nasarar da Najeriya ta samu, inda ta lallasa kasar Australia da ci 6-0 a gasar cin kofin duniya ta matasa ‘yan kasa da shakaru 17 da ake gudanar wa a Chile, yanzu haka kungiyar Golden Eaglet ta Najeriya, za ta kara da Brazil a wasan dab da na kusan karshe a gasar.

Talla

Najeriya wadda ta dauki kokfin gasar har sau hudu, na taka rawar gani, yayin da ta yi nasara a wasanni uku cikin hudu da ta buga.

Ita ma dai Brazil ta samu nasara a wasanni uku cikin hudu da ta buga, kuma za ta kara da Najeriya ne sakamakon doke New Zealand da ta yi da ci daya mai ban haushi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.