FIFA-U17

Najeriya ta doke Brazil a Chile

Nigerian Golden Eaglets defeated Brazil 3-0 in U17 world Cup in Chile
Nigerian Golden Eaglets defeated Brazil 3-0 in U17 world Cup in Chile Thenff twitter

‘Yan wasan Golden Eaglets na Najeriya sun kai zagayen kusa da karshe a gasar cin kofin duniya ta ‘yan kasa da shekaru 17 da ake gudanarwa a Chile, bayan sun lallasa ‘yan wasan Brazil 3 da 0.

Talla

Tun kafin a je hutun rabin lokaci ‘yan wasan Eaglets suka ba Brazil kashi.

Victor Oshimen ne ya fara zira kwallo a raga ana minti 28 da fara kwallo, kuma kwallon shi ta 8 da ya zira a gasar.

Bayan minti guda kuma Kingsley Michaely Michael ya sake jefa kwallo ta biyu. Can daga bisani kuma kafin aje hutun rabin lokaci Udochukwu Anumudu ya zira kwallo ta uku ana minti 34 da wasa.

Yanzu Golden Eaglets za su hadu ne da Ecuador ko Mexico a ranar Alhamis a wasan dab da na karshe wadanda za su kece raini a yau Litinin.

Bidiyon yadda Golden Eaglets suka lallasa Brazil

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI