Wasanni

Infantino zai janye daga takarar FIFA

Gianni Infantino, daya daga cikin masu neman kujerar shugabancin hukumar kwallon kafa ta duniya.
Gianni Infantino, daya daga cikin masu neman kujerar shugabancin hukumar kwallon kafa ta duniya. REUTERS/Denis Balibouse

Dan takarar shugabancin hukumar kwallo kafa ta duniya, Gianni Infantino ya bayyana cewa zai janye daga takarar matukar an  amnice wa Michel Platini, shugaban hukumar kwallon kafar Turai da ya tsaya takara.

Talla

Platini da Sepp Blatter na fuskantar tuhuma sakamakon zargin su da hannu a badakalar cin hanci da rashwa da ta dabaibaye hukumar kwallon kafa ta duniya.

To sai jagororin biyu sun musanta wannnan zargin da ake yi musu.

Ana ganin da yiwuwar FIFA ta amince wa Platini ya tsaya takarar matukar wa’adiun kwanaki casa’in na dakatar da shi ya cika kafin zaben shugaban FIFA a ranar 26 ga watan Fabairun shekara mai zuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI