Boxing

Fury ya zama zakaran damben Boxing na duniya

Tyson Fury ne zakaran Damben Boxing bayan ya doke Wladimir Klitschko
Tyson Fury ne zakaran Damben Boxing bayan ya doke Wladimir Klitschko Reuters

Tyson Fury na Birtaniya ne zakaran damben Boxing na duniya bayan ya doke Wladimir Klitschko a fafatawar da suka yi a jiya Asabar a Jamus. Wannan ne karon farko da aka samu galabar Klitschko a tsawon shekaru 11.

Talla

Yanzu Fury ya karbe kambunan Wladimir Klitschko guda hudu da suka hada da WBA da IBF da IBO da WBO, wanda ya ba shi damar zama zakara a duniya.

Bayan kamala damben, Fury ya bayyana farin cikin shi tare da sadaukar da nasarar da ya samu akan Matarsa.

Klitschko ya sha alwashin kwato kambunsa, idan Fury zai amince su sake dambacewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.