Premier

Liverpool da Arsenal sun tashi ci 3 da 3

Joe Allen ne ya jefawa Liverpool kwallo ta uku a ragar Arsenal
Joe Allen ne ya jefawa Liverpool kwallo ta uku a ragar Arsenal Reuters
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 1

Wasa tsakanin Liverpool da Arsenal an tashi ne ci 3 da 3, Sakamakon da kuma bai yi wa Arsenal dadi ba saboda Leicester City ta samu sa’ar Tottenham ci 1 da 0.

Talla

Joe Allen ne ya kwaci Liverpool a hannun Arsenal wanda ya rama kwallo ta uku ana dab da kammala wasan a jiya Laraba a Anfield gidan Liverpool.

Yanzu Leicester na da maki guda ne da Arsenal da ke jagorancin teburin Firimiya, dukkaninsu da maki 43.

Tazarar maki uku suka ba Manchester City wacce ta buga wasa babu ci tsakaninta da Everton a jiya.

West Bromwich ma ta rike Chelsea ne ci 2 da 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.