Zakarun Turai

Real Marid ta fitar da Roma

Cristiano Ronaldo da James Rodriguez ne suka jefa wa Madrid kwallayenta a ragar Roma.
Cristiano Ronaldo da James Rodriguez ne suka jefa wa Madrid kwallayenta a ragar Roma. REUTERS

Real Madrid da Wolfsburg sun kai zagayen kwata fainal a gasar zakarun Turai bayan sun samu nasara a wasanninsu da suka buga a jiya Talata.

Talla

Real Madrid ta tsallake ne da jimillar kwallaye 4 da 0 bayan ta sake doke Roma ci 2 da 0.

Cristiano Ronaldo da James Rodriguez ne suka jefa wa Madrid kwallayenta a ragar Roma.

A tarihi kuma Wannan ne karon farko da Real Madrid ta samu nasara gida da waje akan wata kungiyar Italiya a gasar Turai a tsawon shekaru 29.

Wolfsburg ta Jamus ma ta tsallake ne da jimillar kwallaye 4 da 2 bayan ta doke Gent Belgium ci 1-0.

A karawa ta farko kungiyoyin biyu sun tashi ne ci 3 da 2.


Wasannin Laraba

Chelsea za ta karbi bakuncin PSG da ke da nasara akanta ci 2 da 1 a yau Laraba

Benfica kuma za ta kai wa Zenit St Petersburg ziyara ne a Rasha.

A karawa ta farko Zenit ta sha kashi ne ci 1 da 0.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.