Zakarun Turai

Barcelona ta doke Atletico Madrid

Kwallaye biyu Suarez ya jefa a ragar Atletico Madrid
Kwallaye biyu Suarez ya jefa a ragar Atletico Madrid REUTERS

Barcelona ta samu sa’ar Atletico Madrid ci 2 da 1 a kwarawar farko a zagayen kwata fainal da suka yi a gasar zakarun Turai a jiya Talata.

Talla

Kusan saura tsawon awa daya a kammala wasan alkalin wasa ya ba Fernando Torres jan kati, bayan ya jefa kwallo a ragar Barcelona ana minti 25 da soma wasa.

Suarez ne ya rama kwallon Torres tare da sake jefa kwallo ta biyu a ragar Atletico Madrid.

Torres ya ce da ba don jan katin da aka ba shi ba da sai sun doke Barcelona.

Tsokacin da Felipe Luis ya yi a wata kafar telebijin din Spain ya ja hankali musamman a Twitter inda ya ce UEFA na tsoron kada Barcelona ta kasa zuwa wasan karshe.

A wani makon ne dai ranar 13 ga wata kungiyoyin biyu zasu sake haduwa a gidan Atletico Madrid.

Bayern Munich da Benfica

Bayern Munich ta doke Benfica ne ci 1 da 0 a karawar farko da suka fafata a Allianz Arena.

Ana soma wasan ne dan kasar Chile Arturo Vidal ya jefawa Bayern Munich kwallonta a ragar Benfica.

Bayan idar da wasan kocin Benfica Rui Vitoria yace wasa bai karewa ba domin a Lisbon komi na iya faruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.