Zakarun Turai

Bayern Munich da Atletico sun kai zagayen dab da karshe

Antoine Griezmann ne ya jefawa Atletico Kwallayenta biyu a ragar Barcelona
Antoine Griezmann ne ya jefawa Atletico Kwallayenta biyu a ragar Barcelona REUTERS

Atletico Madrid da Bayern Munich sun kai zagayen dab da na karshe a gasar zakarun Turai bayan sun samu nasara akan Barcelona da Benfica a wasannin da suka fafata a daren Laraba.

Talla

Atletico Madrid ta yi waje ne da Barcelona mai rike da kofin gasar da jimillar kwallaye 3 da 2.

Bayan sun yi 2 da 1 a gidan Barcelona, a jiya kuma Atletico ta doke Barcelona ci 2 da 0.

Antoine Griezmann ne ya jefa wa Atletico Madrid kwallayenta biyu a ragar Barcelona.

Wannan ne karo na uku da Barcelona ke shan kashi a wasanni 4 tun lokacin da Real Madrid ta karya lagonta na buga wasanni 39 ba a samu galabarta akanta ba.

Kocin Barcelona Luis Enrique ya daura laifin ficewarsu akan shi musamman yadda ya sa babban buri akan kare kofin gasar zakarun Turai da suka lashe a bara.

Bayarn Munich kuma ta kai zagayen dab da na karshe ne da jimillar kwallaye 3-2 akan Benfica.

kungiyoyin biyu sun tashi ci 2 da 2 ne a Lisbon a jiya, amma a karawa ta farko Bayern ta doke Benfica ne ci 1 da 0.

Yanzu Bayern Munich da Altetico Madrid sun bi sahun Real Madrid da Manchester City da suka kai zuwa zagayen dab da karshe.

A ranar Juma’a ne za a hada kungiyoyin guda hudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.