Wasanni

Tottenham ta rage rata tsakaninta da Leicester

Tawagar Tottenham
Tawagar Tottenham

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta lallasa Stoke City da ci 4-0 a karawar da suka yi a jiya a gasar Premier ta Ingila, lamarin da ya bata damar zabtare tazarar makin da ke tsakaninta da Leicester City mai jangorantar teburin gasar. 

Talla

Yanzu haka dai akwai tazarar maki biyar kacal tsakanin kungiyoyin biyu, inda Leicester ke da maki 73 yayin da Tottenham ke da maki 68 kuma Tottenham din nada wasaanni guda hudu da za ta yi nan gaba.

Harry Kane da Dele Alli ne suka ci wa Tottenham kwallaye biyu- biyu a fafatawar ta jiya.

Canjaras din da Leicester City ta yi 2-2 da West Ham ne a shekaran jiya, ya bai wa Tottenham damar zabtare tazarar makin da ke tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.