Isa ga babban shafi
UEFA

Platini ya yi murabus

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai, Michel Platini.
Shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai, Michel Platini. REUTERS/Ruben Sprich/File
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
1 min

Michel Platini ya yi murabus daga mukamin shugaban hukumar kwallon Turai UEFA bayan kotun wasanni ta yi watsi da koken da ya shigar yana kalubalantar hukuncin da FIFA ta yanke na haramta ma shi shiga sha’anin kwallon kafa.

Talla

Kotun ta sassautawa Platiini hukucin dakatar da shi daga shekaru 6 zuwa shekaru 4.

Amma kotun tace ba ta gamsu da hujjojin shi ba akan hallacin kudaden kwangilar da ya karba daga FIFA kimanin dala miliyan biyu.

Bayan rashin samun nasara a kotun, daga karshe Platini yace baya da zabi a yanzu illa ya yi murabus.

Wannan badakalar ce dai ta haramta ma shi yin takarar shugabancin hukumar FIFA a watan Fabrairu.

Platini ya ce zai ci gaba da kalubalantar tuhumar da ake ma shi a kotun Switzerland.

Wannan dai shi ya haramtawa Platini jagorantar wasannin gasar cin kofin Turai da kasar shi Faransa za ta dauki nauyi a watan gobe.

A ranar 18 ga wannan watan na Mayu ake sa ran kwamitin zartarwar UEFA zai gudanar da taro a Basel domin tsayar da ranar zaben wanda zai gaji Platini.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.