Wasanni

Fargaban bam a Old Trafford na Ingila

Filin wasa na Old Trafford da ke Ingila.
Filin wasa na Old Trafford da ke Ingila. belfasttelegraph.co.uk

Wani abu mai kama da bam da aka gano a filin wasa na Old Trafford da ke Ingila ya tilasta wa jami’an ‘yan sanda fitar da ‘yan kallo daga filin wasan.

Talla

A yammacin jiya ne aka gano abun a ban-dakin Old Trafford, lamarin da ya sa aka soke fafatawa tsakanin Manchester United da Bournemouth a gasar Premier.

Kwararrun jami’an tsaro sun yi nasarar tarwatsa abun wanda aka ce, wani kamfanin tsaro ne ya manta da shi bayan ya yi atisaye da karnuka kwanaki hudu gabanin fafatawar da aka shirya gudanar da ita a jiya.

Yanzu dai an dage wasan zuwa yammacin gobe Talata yayin da mahukunta birnin na Manchester suka bukaci a gudanar da bincike kan sakacin da kamfanin tsaron ya yi.

Filin Old Trafford na daukan 'yan kallo dubu 75 da 600.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI