Tennis

Sharapova za ta daukaka kara

Tsohuwar jarumar Tennis Maria Sharapova ta sha alwashin daukaka kara domin kalubalantar dakatar da ita da aka yi na tsawon shekaru biyu kan shan abubuwa masu sa kuzari.

Maria Sharapova ta Rasha
Maria Sharapova ta Rasha REUTERS/Daniel Munoz/File Photo
Talla

An dakatar da ‘yar wasan ta Rasha ne bayan wani gwaji ya nuna tana shan kwayar Meldonium da aka haramta kafin soma gasar Australian Open a watan Janairu.

‘Yar wasan ta yi kakkausar suka ga matakin dakatar da ita, matakin da hukumar Tennis ta duniya tace ya soma aiki tun daga watan Janairu bayan tabbatar da Sharapova sabawa dokokin yaki da shan abubuwa masu sa kuzari a wasanni.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI