Wasanni

Maradona ya bukaci Messi ya janye ritayarsa

Lionel Messi na Argentina ya yi murabus ne saboda takaicin rashn samun nasara
Lionel Messi na Argentina ya yi murabus ne saboda takaicin rashn samun nasara 路透社照片

Tsohon dan wasan Argentina Diego Maradona ya bukaci Lionel Messi da ya janye matakin da ya dauka na yin ritaya daga buga wa kasar kwallon kafa. 

Talla

Messi mai shekaru 29 ya sanar da yin ritayra ne bayan da ya zubar da bugun fanareti a wasan karshe da kasar Chile ta doke su a gasar Copa America, abinda ya bai wa Chile damar sake daukan kofin gasar a karo na biyu a jere.

Maradona ya ce, dole ne Messi ya ci gaba da zama a tawagar Argentina saboda yana da sauran rawar da zai taka wa kasar musamman a gasar cin kofin duniya da za a gudanar a Rasha nan da shekera ta 2018.

A karo na hudu kenan da Messi ke jagorantar kasarsa zuwa matakin wasan karshe a gasar kasa da kasa amma sai ya gaza daukan kofi, abinda ya bayyana a matsayin takaici a gare shi.
 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.