Faransa

Faransa ta kai wasan karshe a gasar Euro 2016

A karon farko cikin shekaru 58 da Faransa ta doke Jamus a wata babbar gasa
A karon farko cikin shekaru 58 da Faransa ta doke Jamus a wata babbar gasa REUTERS/Carl Recine Livepic

Faransa ta kai matakin wasan karshe a gasar cin kofin kasashen Turai da ake yi a kasar bayan ta samu nasarar doke Jamus da ci 2-0 a fafatawar da suka yi jiya a Marseille.

Talla

Antoine Griezmann ne ya ci wa Faransa dukkanin kwallayen biyu kuma a karon farko kenan cikin shekaru 58 da Faransa ta casa Jamus a wata babbar gasa.

Yanzu haka dai Faransa za ta hadu da Portugal a ranar Lahadi mai zuwa, yayin da shugaban kasar Francois Hollande ya bayyana karawar ta ranar Lahadi a matsayin wasa mafi zafi.

Shugaba Holland na cikin manyan bakin da suka halarci filin wasan a jiya, inda ya kalli fafatawar kai tsaye tare da ministan cikin gidan Jamus Thomas de Maizirere.
 

A bangare guda, Anthonie Griezmann ya zama dan wasan da yafi zura kwallaye a wannan gasar ta Euro 2016, inda ya ke da kwallaye 6.

Sai dai ya jinjinawa Michel Platini wanda ya fi kowa zura kwallaye a tarihin gasar cin kofin kasashen Turai, inda ya ke da kwallaye tara.

Platini shi ne wanda ya ci wa Faransa kwallaye tara a irin wannan gasar da aka gudanar a shekara ta 1984 kuma kasar ce ta dauki kofi a wancan lokacin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.