wasanni

NFF ta dauki sabon kocin Najeriya

Sabon kocin Najeriya, Paul Le Guen
Sabon kocin Najeriya, Paul Le Guen AFP PHOTO / Aris Messinis

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta dauki Paul Le Guen dan asalin kasar Faransa domin jagorantar tawagar super Eagles a wasannin neman gubin shiga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018 da za a yi a Rasha.

Talla

Kwamitin tsare-tsare na hukumar NFF ya ce, Salisu Yusuf da ya kula da tawagar na wucen gadi da kuma Imma Amakapabo na Enugu Rangers za su taimaka wa sabon Kocin don ganin Najeriya ta kai ga gaci a fafatawar da za ta yi da Kamaru da Algeria da Zambia da aka hada su cikin rukuni guda.

Mr. Guen dai shi ne wanda ya jagoranci kasar Kamaru zuwa gasar cin kofin duniya ta shekarar 2010, kuma ya horar da manyan kungiyoyin kwallon kafa a Faransa kamar Paris Saint Germaine da Lyon.

Kana ya horar da kungiyar Rangers ta Scotland da kuma tawagar kwallon kafar Oman duk da cewa a shekara ta 2015 ne ya raba gari da tawagar.

Hukumar NFF ta tabbatar cewa za ta rika biyan sabon kocin mai shekaru 52 albashinsa akan kari wanda ya kai Dalar Amurka dubu 50 a kowanne wata, kwatankwacin Naira miliyan 18 da dubu 400 na Najeriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.