Wasanni

An nada Allardyce a matsayin kocin Ingila

Sabon kocin Ingila Sam Allardyce
Sabon kocin Ingila Sam Allardyce Reuters/Russell Cheyne

A yau jumma’a hukumar kwallon kafar Ingila ta tabbatar da Sam Allardyce a matsayin sabon kocin da zai ci gaba da horar da tawagar kasar.

Talla

Allardyce mai shekaru 61 ya kulla kwantiragin shekaru biyu bayan an cimma matsaya da kungiyarsa ta Sunderland wadda ya jagoranta zuwa gasar Premier a kakar da ta wuce.

Yanzu haka kocin zai ci gaba da gudanar da aikin Roy Hodgson da ya yi murabus bayan Iceland ta yi waje da Ingila a gasar cin kofin nahiyar Turai da aka kammala a Faransa.

Ana saran a ranar 1 ga watan Satumba mai zuwa, sabon kocin zai fara jagorantar Ingila a wani wasan sada zumunta da wata kasa da kawo yanzu ba a sanar da ita ba.

Amma a ranar 4 ga watan na Satumba zai sake jogorantar tawagar a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya, inda za su fafata da Slovakia.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.