Brazil

Olympics : Wasannin Rio na cike da kalubale

Ranar Juma'a 5 ga Agusta ake soma wasannin Olympics a birnin Rio na Brazil
Ranar Juma'a 5 ga Agusta ake soma wasannin Olympics a birnin Rio na Brazil REUTERS/Nacho Doce

A ranar Juma’a 5 ga Agusta ake soma wasannin Olympics gadan-gadan mai cike da kalubale a birnin Rio na Brazil. Tun a ranar Laraba aka soma da kwallon kafa kafin bikin bude wasannin.

Talla

Wasannin Rio ya kasance mafi kalubale da aka fuskata a tarihin Olympics, duk da an shafe shekaru 7 ana shiryen shiryen wasannin.

Masu shirya wasannin na fatar bude wasannin na kwanaki 17 kuma a kammala lafiya.
Bude wasannin dai na zuwa ne bayan an fuskanci matsaloli da dama. Matsalolin tattalin arziki da rashin ayyukan yi da rikicin Siyasa a Brazil na ci gaba da zama barazana ga wasannin

Ga kuma annobar cutar Zika a Brazil inda ‘yan wasa da dama suka gujewa zuwa wasannin na Olympics.

Matsalar tsaro ma na cikin manyan kalubale da wasannin na Olympics ke fuskanta inda ‘yan wasan wasu kasashe da suka isa kasar ke kukan ana masu sata.

Gwamnatin Brazil ta baza sojoji da ‘Yan sanda sama da dubu tamanin domin kula da shan’anin tsaro a lokacin wasannin a Rio.

Rahotanni sun ce kasar China ta aika da jami’an tsaro domin kare lafiyar ‘Yan wasanta.

Masu shirya wasannin sun ce akwai tikicin shiga wasannin sama da miliyan guda da suka yi kwante ciki har da wasannin da aka fi yawan shiga a wasannin Olympics irinsu tseren gudun mita 100 a bangaren maza.

A bana dai akwai tawagar ‘Yan gudun hijira da za su fafata a wasannin na Rio.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI