Wasanni

Enugu Rangers ta lashe kofin firimiya ta Najeriya

Enugu Ranger ta lashe kofin firimiya ta Najeriya
Enugu Ranger ta lashe kofin firimiya ta Najeriya

A karon farko cikin shekaru 32, kungiyar kwallon kafa ta Enugu Rangers ta samu nasarar lashe kofin gasar firimiya ta Najeriya wannan kakar. 

Talla

Wannan na zuwa ne bayan ta doke Ikorodu United da ci 2-1 a fafatawar da suka yi a filin wasa na MKO Abiola a jiya lahadi.

Dama dai Wiki Tourist da Rivers United na cikin wadanda aka yi hasashen za su iya lashe gasar, amma suka gaza samun sakamakon da ake bukata.

Domin kuwa Wiki Tourist ta sha kashi a hannun Shooting Stars da ci daya mai ban haushi, yayin da Rivers United ta yi kunnen doki da Abia Warriors.

A jumulce dai, Enugu Rangers na da maki 60 a teburin gasar kuma tana da wasa guda daya da ya rage za ta yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.