Wasanni

West Ham ta sha kashi sau hudu a jere

West Ham ta sha kashi a hannun Southampton a gasar Premier ta Ingila
West Ham ta sha kashi a hannun Southampton a gasar Premier ta Ingila

Kungiyar kwallon kafa ta Southampton ta lallasa West Ham da ci 3-0 a karawar da suka yi jiya a gasar ta Premier ta Ingila.

Talla

A karo na hudu kenan a jere da West Ham ta sha kashi, yayin da kaften dinta, Mark Noble ya bayyana yanayin tsaron bayansu a matsayin abin dariya.

Har dai aka kammala wasan na jiya, sau daya kacal West Ham ta kai kyakkyawan harin cin kwallo, yayin da dubban magoya bayannta suka fice daga filin wasan gabanin a tashi saboda bakin ciki.

A bangare guda, sau biyar kenan da dan wasan Southampton, Charlie Austin ke ci wa kungiyar kwallaye biyar a wasanni hudu da ya buga mata.

Kuma shi ne ya fara zura kwallo a wasan jiya a minti na 40, kafin daga bisani Tadic da Ward-Prowse kowanne ya zura tasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI