Wasanni

An fara gyara wa Super Eagles filin wasa na Uyo

Wasu daga cikin 'yan wasan Najeriya
Wasu daga cikin 'yan wasan Najeriya AFP PHOTO/PIUS UTOMI EKPEI

Hukumomin Najeriya sun fara aikin gyare-gyare a filin wasa na Gods Will Akpabio da ke Uyo gabanin karawar da tawagar kasar za ta yi da  Algeria a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.

Talla

Dama dai hukumar kwallon kafar kasar ta bayar da tabbacin cewa, za ta bukaci gwamnatin jihar Akwa Ibom da ta gyara filin wasan sakamakon korafin da ‘yan wasan Super Eagles suka yi, in da suka koka kan rashin kyawun filin wasan.

‘Yan wasan dai ba su ji dadin yadda suka kara da Tanzania ba a cikin watan jiya a wannan filin a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika saboda rashin kyawun sa.

A ranar 12 ga watan gobe ne dai, Najeriya za ta fafata da Algeria a filin.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.