Isa ga babban shafi
Wasanni

Sissoko zai fuskanci haramcin buga wasanni uku

Dan wasan tsakiya na Tottenham Moussa Sissoko
Dan wasan tsakiya na Tottenham Moussa Sissoko
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 1

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta ce ba zata saka baki kan hukuncin da hukkumar kula da gasar Premier league ta kasar Ingila ta yanke kan dan wasanta Moussa Sissoko ba.

Talla

A wasan da kungiyar Tottenham ta buga Bournemouth Sissoko yayi amfani da gwiwar hannunsa wajen yiwa Harry Arter gula a fuska a wasan da suka tashi canjaras.

Da fari dai tamkar Sissoko zai ci bulus kasancewar alkalan wasa basu ga lokacin da yayiwa Arter mahagurbar ba, sai dag baya aka gano cikin bidiyon da aka nada yayin kallon wasan daga baya.

Yanzu Sissoko zai iya fuskantar hukuncin haramcin buga wasanni uku da ya hada dana yau tsakanin Totttenahm da Liverpool.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.