Isa ga babban shafi
Wasanni

Guardiola ya ce ba zai haska Toure a wasanni ba

Kocin Manchester City Pep Guardiola na takun saka da dan wasan kungiyar Yaya Toure
Kocin Manchester City Pep Guardiola na takun saka da dan wasan kungiyar Yaya Toure Reuters / Michaela Rehle
Zubin rubutu: Umaymah Sani Abdulmumin
Minti 1

Kocin Manchester City Pep Guardiola, ya ce yana nan kan bakarsa, na hana Yaya Toure wasanni saboda kallaman Manajansa, Dimitri Seluk, na cewa kin sanya Toure a tawagar gasar zakaran Turai tamkar cin mutunci ne.

Talla

A yau City zata ziyarci United a gasar league Cup zagaye na 4, kuma Guardiola ya ce muddin Seluk bai nemi afuwa ba, to ba zai haska Toure a wasanni ba.

A cikin watan Satumba kungiyoyin biyu sun kara a gasar Premier a Old Trafford, inda City ta ci United 2-1.

Yaya Toure wanda ke taka rawar gani a City, ya ce ba zai nemi afuwa laifin ba bai aikata ba.

Sauran wasanni a Yau

Southampton v Sunderland

West ham v Chelsea
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.