Isa ga babban shafi
Wasanni

Liverpool ta fitar da Tottenham daga League Cup

Daniel Sturridge ne ya ciwa Liverpool kwallaye biyu a karawar su da Tottenham
Daniel Sturridge ne ya ciwa Liverpool kwallaye biyu a karawar su da Tottenham Reuters
Zubin rubutu: Umaymah Sani Abdulmumin
Minti 1

Liverpool ta fidda Tottenham daga League Cup bayan doke ta da ci 2-1. Daniel Sturridge ne ya ci mata kwalleye guda 2 wanda ya ba ta daman kai wa kwata final, kuma nasara a wasanni 10.

Talla

Duk da irin kokarin da Tottenham ta yi bata samu daman farke kwallaye biyu ba, sai guda daya a bugun Fenareti ta hannu Vincent Janssen

Wannan dai ya kasance karon farkon da Janssen ke zura kwallo a gasar ta league tun bayan siyo shi daga AZ Alkmaar da Mauricio Pochettino ya yi kan fam miliyan 17.

Itama  Arsenal ta doke Reading da ci 2-0 ta hannu Alex Oxlade Chamberlain, kuma Reading ta kusan farke cin ta hannu Callum Harriotts wanda bai samu ba. Yanzu dai wasanni 14 kenan Arsenal ke karawa ba tare da an doke ta ba.

A Sauran wasanni Kuma

Hull City 2-1 Bristol City

Leeds 2-2 Norwich

Newcastle 6-0 Preston

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.