Isa ga babban shafi
Wasanni

Chelsea ta dare mataki na hudu a gasar Premier

Chelsea ta tsallaka mataki na hudu a teburin gasar Premier ta Ingila
Chelsea ta tsallaka mataki na hudu a teburin gasar Premier ta Ingila Reuters / Dylan Martinez Livepic
Minti 1

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta tsallaka mataki na hudu a teburin gasar Premier ta Ingila bayan da ta yi nasarar casa Southampton da ci 2-0 a fafatawar da suka yi jiya lahadi.

Talla

Eden Hazard ne ya fara zura kwallon farko a minti na shida da fara wasan kafi daga bisani Diego Costa ya zura tasa a minti na 55.

Southampton dai ta samu damammakin rike kwallaye amma duk da haka ta gaza ratsa tsakiyar ‘yan wasan Chelsea don jefa kwallo a raga.

A karo na hudu kenan da Chelsea ke samun nasara a jere a gasar Premier ta Ingila, kuma raban da ta samu irin wannan nasarar tun a cikin watan Aprilun shekarar bara.

A yanzu dai tazarar maki guda ke tsakanin Chelsea da Manchester City da Aresenal da Liverpool da ke samanta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.