Wasanni

Ronaldo ya lashe kyautar Ballon d'Or

Gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya Cristiano Ronaldo da ya lashe kyautar Ballan d'Or
Gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya Cristiano Ronaldo da ya lashe kyautar Ballan d'Or

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Cristiano Ronaldo ya yi nasarar lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya ta Ballon d’Or.

Talla

Wannan dai shi ne karo na hudu da Cristiano Ronaldo yake lashe wannan kyauta, bayan da 'yan jaridu daga sassan duniya 173 suka jefa masa kuri’a.

A kakar wasa ta bana, Ronaldo ya samu nasarar jefa kwallaye 48 cikin wasanni 52 da ya bugawa kungiyarsa ta Real Madrid, da kuma kasarsa Portugal.

A baya gwarzon dan wasan, ya taba lashe wannan kyauta a shekarun 2014, 2013, da kuma 2008.

Har yanzu dai dan wasan kungiyar Barcelona Lionel Messi ke kan gaba, wajen lashe kyautar gwarzon dan wasa na duniya, bayan nasarar lashe kyautar har sau 5.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.