Wasanni

An biya Super Falcons na Najeriya kudinsu

'Yan wasan  kungiyar kwallon kafa ta Najeriya mata, Super Falcons
'Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya mata, Super Falcons

‘Yan wasan Super Falcons na Najeriya sun fice daga Otel din Agura da a baya suka ce, ba za su fice ba har sai gwamnati ta biya su kudadensu na alawus bayan sun lashe kofin gasar kwallon Afrika ta mata a Kamaru.

Talla

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya bayar da umarnin a biya ‘yan wasan bayan sun gudanar da zanga-zanga a kofar majalisar tarraya ta kasar da nufin janyo hankalin shugaban da ke halartar majalisar a ranar.

Ministan wasanni da matasa na kasar Barr.Solomon Dalung, ya bayyana wa sashin hausa na RFI cewa, an bai wa kowacce daga cikin matan Naira miliyan 8.

A farko dai, 'yan matann sun jajirce cewa dole ne gwamnati ta biya kowacce daga cikin su kimanin Naira miliyan 11, kudaden da suka hada da bashin  da suke bi a can baya da kuma na yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.