Wasanni

Senagal ta lashe gasar kwallon kafa ta yashi

Tawagar 'yan wasan kasar Senegal da suka lashe kofin gasar kwallon kafar bakin teku ta nahiyar Afrika
Tawagar 'yan wasan kasar Senegal da suka lashe kofin gasar kwallon kafar bakin teku ta nahiyar Afrika

Kasar Senegal ta lashe kofin gasar kwallon kafar bakin teku ta nahiyar Afrika ta shekarar 2016, bayan lallasa Najeriya wadda ita ce mai masaukin baki, wato Super Sand Eagles.

Talla

Senegal ta samu wannan nasara bayan lallasa Najeriya da kwallaye 8-4, a wasan karshe da suka fafata shi a Eko Atlantic da ke jihar Legas a kasar.

Karo na hudu kenan da Senegal ke lashe kofin gasar, yayinda Najeriya ta taba lashe kofin a shekarun 2003 da kuma 2007

Sai dai kuma a wani cigaban, kasashen biyu ne zasu wakilci nahiyar Afrika a gasar cin kofin kwallon yashi da ake yenta a bakin teku ta duniya, da kasar Bahamas zata karbi bakunci a shekara ta 2017.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.