Wasanni

Liverpool ta samu karin maki a gasar Premier

Sadio Mané ya taimaka wa Liverpool samun karin maki uku a gasar Premier
Sadio Mané ya taimaka wa Liverpool samun karin maki uku a gasar Premier GEOFF CADDICK / AFP

Kungiyar kwallonn kafa ta Liverpool ta doke Everton da ci daya mai ban haushi a fafatawar da suka yi jiya a gasar Premier ta Ingila. 

Talla

Kungiyoyin biyu sun shafe mintina 90 ba tare da jefa kwallo a raga ba, yayin da Sadio Mane na Liverpool ya yi nasarar jefa kwallon daya tilo bayan an kara musu lokaci.

Sau daya ne kacal da Everton ta doke Liverpool a cikin wasanni 20 da kungiyoyin biyu suka yi a baya-bayan nan.

Yanzu haka dai Liverpool ta samu karin maki uku amma akwai tazarar maki shida tsakaninta da Chelsea da ke jan ragama a teburin gasar Premier da maki 43.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.