Wasanni

Senegal ce ke jan ragamar jadawalin FIFA a Afirka

Tawagar 'yan wasan Sénégal
Tawagar 'yan wasan Sénégal AFP PHOTO/MONIRUL BHUIYAN

Hukumar Fifa ta fitar da jadawalin kasashen da suka fi iya taka leda a duniya, kamar yadda ta sa ba lokaci zuwa lokaci,a Nahiyar Afrika Senegeal ce ke kan gaba a wannan lokaci, inda ta doke Ivory Coast da ke rike da kambun Nahiyar Afrika.

Talla

Jawadalin da ta fitar na wannan Disambar, ya ce Senegal ce ta farko kuma ta 33 a Duniya, yayin da Ivory coast ke bi mata a mataki na Biyu kuma na 34 a duniya.

Tunisia ce ta Uku a Afrika sai Masara ta 4, Algeria ta 5, DR Congo ta 6, Burkina Faso ta 7, Najeriya ce ta 8 kuma ta 51 a duniya, sai Ghana da ke na 9 a Afrika ta 53 a Duniya, Moroko ke matakin na 10 a jadawalin.

Dukkanin wadanan kasashe dai na cikin kasashe 16 da zasu fafata da junan a gasar cin kofin nahiyar Afrika da Gabon za ta dauki nauyi tsakanin 14 ga watan Janairu zuwa 5 ga watan Fabiru mai zuwa a birnin Libreville.

A duniya gaba daya kuwa Argentina ta ci gaba da zama ta daya a jerin gwanayen tamaular.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.