Kwallon Kafa

Wata kungiyar China ta taya Ronaldo Fam miliyan 250

Cristiano Ronaldo ya lashe kyautar Balon d'Or a bana
Cristiano Ronaldo ya lashe kyautar Balon d'Or a bana Reuters/Sergio Perez

Wata kungiya a China ta taya Cristiano Ronaldo na Real Madrid akan kudi fam miliyan 250 kamar yadda wakilin shi ya tabbatar. Sannan kungiyar da ba a bayyana sunanta ba ta yi alkawalin ba dan wasan albashin kudi fam miliyan 85 a shekara.

Talla

Sai dai Jorge Mendes wakilin na Cristiano ya ce dan wasan ba ya bukata, duk da cewa kungiyar ta China ta ce za ta dinga biyan shi kudi fam miliyan daya da dubu dari shida a mako, kudaden babu mai karba a duniya.

“Kudi ba komi ba ne”, a cewar Mendes, wakilin na Ronaldo.

Ba a jima ba dai da zakaran kwallon kafar na duniya ya tsawaita kwangilar shi da Real Madrid inda zai ci gaba da murza kwallo har shekarar 2021.

Jorge Mandes ya ce Real Madrid ta kasance rayuwar Cristiano Ronaldo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.