CAF

Mahrez ne gwarzon Afrika

L'Algérien Riyad Mahrez.
L'Algérien Riyad Mahrez. Courtesy of CAF

Riyad Mahrez ne na Algeria ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na Afrika bayan ya samu kuri’u fiye da dan kasar Gabon Pierre-Emerick Aubameyang da ya lashe kyautar a bara.

Talla

Mahrez dai ya taka rawar gani ga nasarar da Leicester City ta samu na lashe kofin Firimiya inda kuma ya jefa kwallaye 17.

Pierre-Emerick Aubameyang na Borussia Dortmund ne ya zo a matsayi na biyu sai Dan wasan Liverpool Sadio Mane na Senegal ya zo a matsayi na uku a bikin da aka gudanar a birnin Abuja na Najeriya

A bangaren mata ‘yar kwallon Najeriya da ke wasa a Arsenal Asisat Oshoala ceta lashe kyautar, kuma karo na biyu ke nan tana lashe kyautar bayan ta karba a 2014.

Kungiyar Super Falcons na Najeeiya ne aka ba kyautar babbar kungiya a Afrika, bayan lashe kofin afrika na Mata a kamaru a bana. A bangaren Maza Uganda ce ta karbi kyautar.

Kwalkifan Memolodi Sundown da ta lashe kofin Zakarun Afrika aka ba gwarzon dan wasan Afrika da ke taka kwallo a gida.

‘Yan wasan Najeriya Kelechi Iheanacho na Manchester City da Alex Iwobi na Arsenal ne suka lashe kyautar gwarzaye masu tasowa.

Bakary Papa Gassama ne ya lashe kyautar gwarzon alkalin wasa a karo na uku a jere da jere

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.