Wasanni

Christiano Ronaldo ya lashe kyautar FIFA

Gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya Cristiano Ronaldo da ya lashe kyautar Ballan d'Or da kuma kyauat FIFA
Gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya Cristiano Ronaldo da ya lashe kyautar Ballan d'Or da kuma kyauat FIFA

Gwarzon dan wasan Real Madrid Christiano Ronaldo ya lashe kyautar FIFA ta dan wasan da ya fi fice a shekarar 2016.

Talla

Dan wasan mai shekaru 31 ya doke abokin hamayyarsa na Barcelona Lionel Messi da kuma Antoine Griezmann na Atletico Madrid da suka yi takarar neman lashe kyautar a yau Litinin  a birnin Zurich.

Ronaldo dai shi ne ya lashe kyautar Ballon d'Or a bana bayan ya taimaka wa Real Madrid daukan kofin gasar zakarun Turai.

Sannan kuma ya jagoranci kasar ta asali wato Portugal wajen lashe gasar cin kofin kasashen Turai.
 

Kocin Leicester City Claudio Raneiri ne ya lashe kyautar kocin da ya fi shahara a bara sakamakon rawar da ya taka wajen taimaka wa kungiyar lashe gasar Premier ta Ingila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.