FIFA

FIFA za ta zabi gwarzon duniya

Kyautar gwarzon dan wasan duniya na FIFA
Kyautar gwarzon dan wasan duniya na FIFA Fifa.com

A yau ne hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA za ta zabi gwarzon dan wasan duniya a birnin Zurich tsakanin Cristiano Ronaldo na Real Madrid da Lionel Messi na Barcelona da Antoine Griezmann na Atletico Madrid.

Talla

Wannan ne karon farko da FIFA za ta fara bayar da kyautar bayan warware kawancenta da mujallar Faransa inda a baya ake bayar da kyautar na hadin guiwa da ake kira FIFA Ballon d’Or.

Cristiano Ronaldo da ya karbi Ballon d’Or, a bana shi kuma ake hasashen zai karbi kyautar ta FIFA bayan lashe kofin zakarun Turai a Real Madrid da kuma kofin Turai da ya lashewa Portugal.

Ronaldo dai ya doke Messi a Balon d’Or da Antoine Griezmann na Atletico Madrid kuma tuni jaridun Turai suka kwarmato cewa ya sake buge su a kyautar ta FIFA da za a bayar a yau.

FIFA kuma za ta zabi gwarzon koci tsakanin kocin Real Madrid Zinaden Zidane da Claudio Ranieri da ya jagoranci Liecester City ga daukar kofin Firimiya na Ingila da kuma kocin Portugal Fernando Santos.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.