Wasanni

Najeriya ta yi watsi da daukan nauyin gasar AFCON

Shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika Issa Hayatou
Shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika Issa Hayatou FABRICE COFFRINI / AFP

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta yi watsi da bukatar hukumar kwallon kafa ta Afrika dangane da daukan nauyin gasar cin kofin nahiyar ta ‘yan kasa da shekaru 17 a cikin wannan shekarar.

Talla

A makon jiya hukumar CAF ta janye izinin da ta bai wa Madagascar na daukan nauyin gasar ba tare da tuntubar wata kasa ba da za ta cire mata kitse a wuta kafin janye izinin Madagascar.

Wasu majiyoyi sun ce, a ranar Litinin da ta gabata ne hukumar CAF ta aike da wasika ga NFF ta Najeriya, in da ta bukaci daukan nauyin gasar amma nan da nan NFF da ke fama da matsalolin kudi ta ki amince wa da bukatar.

Masharhanta kan kwallon kafa na ganin cewa, an janye izinin Madagascar ne sakamakon takarar da shugaban hukumar kwallon kafar kasar Ahmed Ahmed zai yi da shugaban hukumar CAF Issa Hayatou a zaben da za a gudanar a cikin watan Maris mai zuwa.

Ana ganin Ahmed na iya yi wa Hayatou da ya dare kan shugabancin CAF tun shekarar 1998 barazana a zaben mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.