CAF

Gabon 2017: Senegal ta doke Zimbabwe

Dan wasan Senegal Moussa Sow
Dan wasan Senegal Moussa Sow RFI/Pierre René-Worms

Senegal ta doke Zimbabwe ci 2 da 0, wanda ya ba ta damar zama kasa ta farko da ta tsallake zuwa zagayen kwata fainal bayan ta samu makin da ta ke bukata a wasanni biyu a gasar cin kofin Afrika da ake gudanarwa a Gabon.

Talla

Senegal ta jima tana shan wahala a gasar cin kofin Afrika, inda tun a tashin farko ake yin waje da ita, Tun 2006 da ta kai zagayen kusa da karshe.

Yanzu kuma Senegal ita ke jagorancin teburin rukuninsu na B.

Tunisia kuma ta doke Algeria ne 2-1. Nan gaba Tunisia za ta hadu ne da Zimbabwe, yayin da Senegal zata kara da Algeria.

A gobe Ghana na iya samun makin da zai ba ta damar tsallakewa zuwa zagayen kwata fainal idan har ta doke Mali a rukuninsu na D.

Sai dai kuma Ghana na iya shan mamaki a hannun Mali wacce ta rike Masar babu ci a karawar farko da suka yi.

Masar da Mali zasu nemi nasarar farko ne a gasar idan har Masar ta doke Uganda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.