Gabon

Kocin Algeria Leekens ya yi murabus

Georges Leekens tsohon Kocin Algeria
Georges Leekens tsohon Kocin Algeria AFP PHOTO / KHALED DESOUKI

Kocin Algeria Georges Leekens ya yi murabus bayan fitar da kasar tun a zagayen farko a gasar cin kofin Afrika a da ake gudanarwa a Gabon. An fitar da Algeria ne ba tare da kasar ta ci wasa guda ba.

Talla

Algeria na cikin kasashen da ake ganin zasu bada mamaki a Gabon, amma kuma ba yi abin azo a gani ba.

Senegal ta rike Algeria ne ci 2-2 a fafatawar da suka yi a jiya Litinin, sakamakon da ya ba Tunisia nasarar tsallakewa zuwa zagaye na biyu bayan ta lallasa Zimbabwe 4-2.

Hukumar kwallon Algeria ce ta tabbatar da murabus din kocin a sanarwar da ta wallafa a shafinta na intanet.

Yanzu Burkina Faso za ta hadu ne da Tunisia a kwata fainal a ranar 28 ga wata. Senegal kuma da Kamaru a washegari 29 ga wata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.