Tennis

Australian Open: Venus da Serena Williams za su hadu a wasan karshe

Serena Williams za ta hadu da Venus Williams a wasan karshe a gasar Australian Open a ranar Asabar
Serena Williams za ta hadu da Venus Williams a wasan karshe a gasar Australian Open a ranar Asabar REUTERS

Serena Williams da ke harin lashe kofin manyan gasannin Tennis, Gram Slams 23 za ta hadu da ‘yar uwarta Venus Williams a wasan karshe a gasar Australian Open da ake gudanarwa a birnin Melbourne.

Talla

‘Yan gidan Williams din za su hadu ne a tsakaninsu a karo na 9.

Venus ta kai zagayen karshe gasar Australian Open a karon farko tun 2009 bayan ta doke Coco Vendeweghe a wasan kusa da karshe, yayin da Serena ta doke Mirjana Lucic-Baroni ta Croatia.

Venus ta kasance ‘yar wasan Tennis mai yawan shekaru da ta kai zagayen karshe a manyan gasannin Tennis na duniya.

A yau ne Roger Federer zai fafata da takwaransa na Switzerland Stan Wawrinka a wasan kusa da karshe. Rafael Nadal kuma zai fafata ne da Grigor Dimitrov.

Wasan karshe dai zai iya kasancewa tsakanin Rafael Nadal da Roger Federer zaratan tennis na duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.