CAF

Gabon 2017: Masar ta doke Ghana, an fitar da Mali da Uganda

Masar ta doke Ghana ci 1-0
Masar ta doke Ghana ci 1-0 Justin TALLIS / AFP

Masar ta doke Ghana ci 1 da 0 a kawarar da suka yi jiya a gasar cin kofin Afrika da ake gudanarwa a Gabon. Amma dukkaninsu sun tsallake zuwa zagayen kwata fainal.

Talla

An yi fitar da Mali da Uganda wadanda suka tashi kunnen doki a karawar da suka yi a jiya.

Masar ce ta jagoranci teburin rukuninsu na D da maki 7, Ghana kuma ta tsallake ne da maki 6.

Yanzu Masar za ta hadu ne da morocco a ranar lahadi a wasan kusa da karshe. Ghana za ta hadu ne da Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo.

A ranar Asabar ne Burkina Faso za ta kara da Tunisia. Senegal kuma da Kamaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.