Wasanni-Spain

"Lokaci yayi da zan ajiye aiki" – Enrique

Mai horar da kungiyar Barcelona Luis Enrique
Mai horar da kungiyar Barcelona Luis Enrique theapricity.com

Mai horar da kungiyar Barcelona Luis Enrique ya ce a karshen kakar wasa ta bana zai ajiye aikinsa domin yana bukatar samun hutu.

Talla

Enrique ya bayyana hakane yayin zantawa da ‘yan jaridu bayan wasansu na jiya inda Barcelonan ta lallasa Sporting Gjion da ci 6-1.

A gefe guda kuma, Enrique ya ce kungiyar Barcelona zata cigaba da dogaro da Lionel Messi wajen fitar da kansu kunya yayinda suka shiga runtsi.

A cewar mai horar da Barcelona, ba laifi bane wata kungiyar kwallon kafa ta bayyana dogaronta kan wani dan wasa muddin karansa ya kai tsaiko kamar gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya har sau biyar, Lionel Messi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.