Wasanni

Matsayin Najeriya a gasar cin kofin kwallon kafar bakin teku ta Duniya

Tawagar yan wasan kwallon kafa na bakin teku na Najeriya
Tawagar yan wasan kwallon kafa na bakin teku na Najeriya http://nigeriannewsdirect.com

An sanya Najeriya cikin rukunin B a gasar cin kofin kwallon kafar yashi ko ta bakin tekku ta duniya da za’a yi cikin wannan shekara a Bahamas.

Talla

Kunshe cikin rukunin da Najeriya ke ciki akwai Italiya, da kuma Mexico sai kuma wata kasar daga nahiyar Asiya da kawo yanzu hukumar FIFA bata bayyana ba.

Karo na biyar Kenan da Najeriya ke samun halartar wannan gasa ta cin kofin kwallon kafar Yashi ta duniya.

A shekarun 2011 da kuma 2007 Najeriya ta samu nasarar kai wa zagayen kusa da kusa dana karshe wato Quarter finals kenan a gasar.

Rukunin farko na gasar kwallon yashin ya kunshi Senegal, mai masaukin baki , Bahamas kenan, Ecuador da kuma Switzerland.

A ranar 27 ga watan Afrilu za’a fara gasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.