Wasanni-Ingila

Pogba ya kafa tarihi a gasar Premier

Dan wasan tsakiya na kungiyar Manchester United Paul Pogba ya zama dan wasa na farko a kakar wasan Premier ta kasar Ingila a bana, da ya samu nasarar rarraba kwallo (passing turance) har sama da 1000 yayin murzawa kungiyarsa leda.

Paul Pogba yayin murnar zura kwallo tare da Jesse Lingard
Paul Pogba yayin murnar zura kwallo tare da Jesse Lingard flipboard.com
Talla

Wani sakamakon bincike da masana masu bibiyar kwallon kafar Ingila, ya nuna cewa, Pogba ya rarraba kwalo har sau 1029 yayin karawa da abokan hamayya.

Zalika matakin kwarewar Pogba wajen bada kwallo yayin wasa ya kai matakin kashi 83.05 cikin dari.

Jordan Henderson na kungiyar Liverpool ke biyewa Pogba da samun nasarar rarraba kwallo har sau 987 yayin yi wa kungiyarsa wasa. Mesut Ozil na Arsenal ke a matsayi na uku da yiwa kwallon kafa rabo na dalla dalla tsakanin ‘yan wasa yayin karawa da abokan hamayya sau 954.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI